1 Nuwamba 2021 - 14:28
​Lebanon: Masar Zata Kammala Aikin Hada Lebanon Da Bututun Gas Zuwa Karshen Shekara

Ministan man fetur na kasar Masar Tarek El-Molla ya bayyana cewa kasar Masar zata kammala aikin hada kasar Lebanon da bututun iskar gas na kasar zuwa karshen wannan shekara, wato nan da watanni biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Egypt Today ta kasar Masar ta bayyana cewa a ranar 8 ga watan Satumban da ya gabata ne ministocin harkokin waje na kasashen Lebanon, Masar Jordan da Siriya suka gudanar da taro a birnin Amman na kasar Jordan inda suka amince da kaiwa kasar Lebanon iskar gas wanda bututunsa zai ratsa kasashen Jordan da Siriya.

Kafin haka dai jakadiyar kasar Amurka a Lebanon ya fadawa shugaban kasar Michel Awun kan cewa Amurka zata taimaka a kawowa kasar Lebanon gas daga kasar Masar bayan da kungiyar Hizbullah ta kasar ta sami nasarar shigo da makashi kasar daga kasar Iran.

342/